Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Miyatti Allah Tayi Allah Wadai Da Matakin Gwamnatin jihar Ekiti Na Hana Kiwo


Wasu makiyaya na kallon ramammun dabbobin su, na kalace-kalacen abinci a kasa a wata kasuwar Dakoro a kasar jamahuriyar Nijer.
Wasu makiyaya na kallon ramammun dabbobin su, na kalace-kalacen abinci a kasa a wata kasuwar Dakoro a kasar jamahuriyar Nijer.

Kungiyar makiyaya ta Miyatti Allah a Najeriya ta koka akan matakin da tace gwamnatin jihar Ekiti ta dauka na haramtawa makiyaya kiwo a fadin jihar.

Taron manema labarai kungiyar Miyatti Allah ta kira a Minna ta jihar Neja, domin mayar da martani akan wannan mataki akan matakin na gwamnatin jihar Ekiti, mataimakin shugaban kungiyar Alhaji Husaini Boso, yace gwamnan jihar Ekiti ne da kansa idan yana tafiya a mota yaga Shanu yake tsayawa ya bayar da umarnin a harbi Shanun, hakan ta faru a gaban makiyaya.

Yanzu haka dai kungiyar ta dauki matakin rubutawa duk hukumomin da suke da hakki domin ganin an dauki matakin da ya kamata a cewar mataimakin shugaban kungiyar ta kasa.

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin gwamnan jihar Ekiti, amma yaci tura. Sai dai bayanai sun nuna cewa wata sabuwar doka ce gwamnatin jihar ta samar domin takaita makiyaya kiwo a jihar, domin kawo karshen barnar da gwamnatin jihar tace makiyayan na haddasawa.

Masanin Shari’a a Najeriya, Barista Dan Lami Wushishi, yace bai kamata ba ace gwamnan jiha da kansa yana fitowa kan titi yana aikata hakan, domin zai yana baiwa ‘yan zauna gari banza ‘yancin fitowa suna farma Shanun mutane. A cewar Barista babu wata dokar kasa da ta tanadarwa gwamnan yin hakan.

Domin karin bayani ga rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

XS
SM
MD
LG