Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Miyetti Allah Bata Amince Da Dokar Hana Kiwo Na Gwamnatin Jihar Benue Ba


Ba Fulatani da Shanu
Ba Fulatani da Shanu

Dokar hana kiwo na Gwamnatin jihar Benue a maimakon gyara hakkan zai kawo mummunar barna ne.

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta nuna rashin amincewa da dokar da majalisar dokokin jihar Benue, a arewa ta tsakiyar Najeriya, ta kaddamar data hana makiyaya kiwo a dazuzzukar jihar in banda kebatattun filaye da masu kiwo suka mallaka.

Sakataren kungiyar Baba Ganjarma, ya shedawa manema labarai a Abuja cewa dokar zata yi karan tsaye ga lamuran kiwo da zaman tare a yankin.

Ganjarma ya kara da cewa dokar zata datse burtalin Shanu da ya ratsa ta jihar ta inda Makiyaya ke bi su tafi kudancin Najeriya,

Sakataren kungiyar ya kara da cewa dokar ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ya kawowa kungiyar damuwa saboda haka kungiyar zata dauki duk matakin da doka ta tanada ganin cewa wannan doka bata yi aiki ba.

Yana mai cewa dokan kanta tayi karo da tsarin mulki na tarayya wanda ya baiwa kowane dan kasa ya tafi ya kuma zauna a koina a tarayyar Najeriya, ba tare da tsangwama ba in dan aka aiwatar da dokokin maimakon kawo gyara sai ya kawo barna.

Baba Ganjarma, ya yi kira ga duk hukumar da ta dace da ta ja hankalin gwamnatin jihar Benue, akan wannan doka da ta aiwatar domin magance shi cikin gaggawa shine zai kawo kyakkyawan fahimta da mashala a kasar.

Kungiyar ta yabawa jihar Bayelsa, da ta ware kadada dubu daya da dari biyu domin makiyaya da nuna takaicin yadda jihar Benue dake tsakiyar makiyaya wanda yake tarihin huldan Tivi da Fulani, amma majalisar dokokin jihar ta kafa dokar.

Gwamnan jihar ta Benue Samuel Ortom, ya koka da wani hari da aka kai a jihar da mutanan sa ne kawai aka kashe in hakkan bai shafin ran kowane makiyaye dokar ta hana kiwo ta tsara daurin shekaru uku ga wanda ya keta ta haka nan za a ci tarar kowace Saniya Naira dubu dari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG