Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Afrika zata kara yawan dakarun kiyaye zaman lafiya a Somalia


Kungiyar Tarayyar Afrika zata kara yawan dakarun wanzar da zaman lafiya da take da su a kasar Somalia.

Shugabannin kasashen Afrika sun bayyana damuwa ainun dangane da hare haren bom da aka kai Kampala cikin wannan watan da ya yi sanadin mutuwar mutane saba’in da shida sun amince jiya Talata cewa nan ba da dadewa ba zasu kara yawan rundunar wanzar da zaman lafiya ta KTA da ake kira AMISOM a Somalia zuwa kimanin dubu goma. A halin yanzu dakarun sun kunshi sojojin Uganda da Burundi dubu shida da dari daya.

Karin dakarun da za a tura zasu haa da sojojin kasar Guinea da kuma sojoji da dama daga Djibouti. Dukansu kasashe ne da musulmi suka fi rinjaye. Duk da yake ba a fayyace abinda aikin rundunar ya kunsa ba, shugaban KTA wanda kuma ya kasance shugaban kasar Malawi Bingu wa Mutharika ya ce kwamandojin AMISOM suna da sabon ikon maida martani kan hare haren da kungiyar al-Shabab ke kaiwa.

Omar al-Bashir na Sudan
Omar al-Bashir na Sudan

Taron ya kuma yi kira ga kwamitin sulhu na MDD ya sa baki dangane da takardar sammacen da aka bayar kan shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir na tsawon shekara guda. An sami rarrabuwar kawuna tsakanin shugabannin nahiyar dangane da takardar sammacen. Da dama daga cikin shugabannin suna goyon bayan kiran da ake yi na kama shugaban kasar Sudan tare da bayyana cewa ci gaba da jinkirta kama shi goyon bayan mai laifi ne. Duk da haka shugabannin sun nemi zauren Majalisar Dinkin Duniya ya janye takarar sammacen da watanni goma sha biyu domin ba kungiyar damar gudanar da bincike. Kotun bin kadin laifuka ta kasa ka da kasa tana zargin shugaba Bashir da aikata laifukan yaki da kisan kiyashi dake da nasaba da yakin Darfur. MDD ta kiyasta cewa kimanin mutane dubu dari uku suka mutu tunda yaki ya barke a yankin farkon shekara ta dubu biyu da uku.

XS
SM
MD
LG