Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Tatasan Musulmi


Kungiyar Wanzar da zaman lafiya ta matasan Musulmi ta na kan yada akidojin zaman lafiya bisa ga koyarwar addinin Musulunci tare kuma da taimakwa dalibai

Wata kungiyar da aka kafa ta don wanzar da zaman lafiya kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, ta bayar da kyaututtukan yabo ga wasu da su ka yi fice wajen kokarin tabbatar da zaman lafiya. Ta kuma ba da wasu komfutoci ga wasu dalibai.

Da ya ke bayani ma wakilinmu a jihar Naija, Mustapha Nasiru Batsari, Shugaban kungiyar, Malam Nura Hashimu ya ce manufar kungiyar ita ce ta cusa sha'awar zaman lafiya a zukatan al'umma ta wajen karrama wadanda su ka taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

Wasu da su ka amfana da kungiyar sun yaba mata da kokarin inganta daawah ta hanyoyin da Musulunci ya amince da su masu tabbatar da zaman lafiya. Haka zalika, wasu dalibai sun ce komfutocin da aka ba su za su taimaka wajen daukaka ilimi.
XS
SM
MD
LG