Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Da Daidaikun Mutane Na Kan Shirin Jaddada Yaki Da Kanjamau


Attajirin nan na Amurka Bill Gates da Ministar Kudin Nijeriya Ngozi Iweala a wani zama na yaki da cutar Kanjamau.
Attajirin nan na Amurka Bill Gates da Ministar Kudin Nijeriya Ngozi Iweala a wani zama na yaki da cutar Kanjamau.

Ana kan haramar gagarumin yaki da cutar kanjamau a gobe Lahadi, ita ce zagayowar ranar jaddada yaki da cutar da kuma kulawa da masu dauke da cutar.

A yayin da ake ta shirye-shiryen jaddada yaki da mugunyar cutar nan ta kanjamau a gobe Lahadi, wadda ita ce zagayowar ranar dada jaddada yaki da cutar da kuma maida hankali kan muhimmancin kulawa sosai da masu dauke da cutar a duniya baki daya, Shugaban Hukumar Yaki Da Kanjamau Da Tarin Fuka Da Malariya Ta Jihar Bauchi, Dr. Abdul'aziz Manga ya ce a gobe hukumar da wasu kungiyoyi da daidaikun jama'a za su ba da himma wajen yin yekuwar kiraye-kirayen jama,a su fito a gwada su don su san matsayinsu dangane da wannan cutar.

Da ya ke amsa tambayoyi daga Halima DJimrao, Dr Manga ya ce idan mutun ya san matsayinsa game da wannan cutar, to ko da an same shi da ita, akwai fa'ida sosai saboda idan aka fara shan magani da wuri za a iya cin karfin cutar har da kashi 90%. Don haka ya ce za su yi kokarin gwada mutane akalla dubu shida (6,000). Ya ce za su yi amfani da kayan fadakarwa sosai don ganar da jama'a.

To amma Dr. Manga ya ce an sami cigaba sosai a yakin da ake da cutar saboda cutar ta ragu zuwa 2.1% daga yadda ta ke a 6.8% a shekara ta 2001 a jihar ta Bauchi. Ya ce a matakin Tarayya ma an sami saukin cutar saboda ta ragu zuwa kashi 4%. Dr. Manga ya ce za su dau sati guda su na yekuwar yaki da cutar da kuma nuna ma mutane muhimmancin nuna kauna da kulawa ga masu dauke da cutar a maimakon
nuna masu kyama.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG