Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi da Daidaikun 'Yan Nijeriya na Kiran a Yi Zaben Nijeriya Cikin Inganci da Adalci


Buhari da Jonathan.
Buhari da Jonathan.

Ganin babban zaben Nijeriya ya kusatowa, 'yan Nijeriya na kara kiraye-kirayen a yi zabe da kyau kuma cikin adalci da gaskiya.

A sa’ilinda babban zaben Nijeriya ke kara matsowa, daidaiku da kungiyoyin ‘yan Nijeriya na kara bayyana ra’ayoyinsu kan abubuwan da su ke ganin ya kamata ‘yan takara na dukkan matakai su kuduri aniyar warwarre su a maimakon a rinka kampe kan abubuwa iri guda, wadanda aka sha yin alkawarin magance su a baya amma har hanzu ba a yi ba.

Shugaban kungiyar sauraron shirye-shiryen gidajen rediyo (Program Media Observers) Malam Baba Iyali Kawu ya ce ya kamata kafin mai zabe ya kada kuri’arsa ya duba ya ga ko me wanda zai zaba din ya yi a baya, bisa ga irin damar da ya samu. Ya ce bai kamata mai zabe ya kada kuri’a ma dan takara don kawai ya hada wani abu kamar addini ko kabila da shi ba. Ya ce ya kamata a ce Nijeriya ta zarce matakin yin kampe da alkawarin samar da ruwa ko wuta da sauransu. Shi kuwa malam Yusuf Usama na Kungiyar Muryar Talaka, kira ya yi ga matasa su je su karbi katunansu na dindindin don su kada kuri’a ga wanda su ke ganin zai kawo masu cigaba. Shi kuwa Yunusa Adamu Muhammad na Kungiyar Rai Dangin Goro kira ya yi ga hukumar zabe ta gudanar da komai yadda ya kamata cikin adalci da gaskiya

Su ma ‘yan siyasa da masana kira su ka yi cewa lallai-lallai a tabbatar da adalaci don a samu zaman lafiya a Nijeriya. Sun yi nuni da abubuwan da su ka faru a baya ta yadda ba a ji da dadi ba.

Kungiyoyi da Daidaikun 'Yan Nijeriya na Kiran a Yi Zaben Nijeriya Cikin Inganci da Adalci - 3'40"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG