Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Kungiyoyi Na Taron Fadakar da Jama'a Akan Zaman Lafiya


Wasu 'yan siyasa
Wasu 'yan siyasa

Kungiyoyi da dama na kokarin ganin ba'a yi tashin hankali ba lokaci da bayan zabe mai zuwa.

Kungiyoyi masu zaman kansu a karkashin kungiyar Plateau Popular Participation and Good Governance Group sun gudanar da taron bita na yini guda akan tabbatar da gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba.

Taken taron shi ne "Babu tashin hankali sai zaman lafiya kadai". Taron ya tattaro shugabannin mata, matasa, al'umma da na addinai.

Taron ya tattauna ne kan matakan da za'a bi wajen gudanar da zaben bana ba tare da samun salwantar rayuka ba kamar yadda aka yi a lokutan baya.

Mr. Akin Omoware jami'in wata kungiya GIZ ta kasar Jamus wadda ta shirya taron bitan yace makasudin taron shi ne su janyo hankulan jama'a kan su gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana. Yace bama son tashin hankali duk da yake wasu ba zasu gamsu da sakamakon zaben ba kuma ba zasu ji dadi ba. To amma akwai matakan yadda za'a kai korafi da ya kamata a bi.

Omomware yace kisan mutane ba zai magance lamarin ba. Hajiya Lantana Abdullahi shugabar wata kungiya tace suna son mutane su san cewa lokacin zabe ba lokacin fada ba ne. Duk abun da za'a yi ana son zaben ya kawo cigaba ba koma baya ba. Suna janwo hankalin matasa su sani cewa kuri'arsu ita ce karfinsu ba fada ba. Kowa ya kada kuri'arsa ba tare da musgunawa wani ba ko tada hankalin jama'a.

Wata Rahab David ta kungiyar kare hakin dan adam tace suna son a samu zaman lafiya lokacin zabe da bayansa domin abun da zaman lafiya bai bayar ba ko an yi rikici ba zai bayar ba. Matasa su sani cewa idan an yi rikici wadanda suka ci zaben zasu je su ji dadi da iyalansu ba tare da damuwa da wadanda aka kashe ba ko aka raunata. Talaka ne ake kashewa shi ne kuma yake asarar dukiya. Yakamata a duba wanene zai yiwa kasar aiki ba bangaranci ba ko nuna banbancin addini da na kabila.

Malam Muhammad Hashim Sa'id wanda ya wakilci matasan musulmi a taron yace sau da dama matasa ne akan yi anfani dasu saboda basu da aikin yi ko sana'a. Suna zaune kara zube. Sai 'yan siyasa su debesu su basu wasu 'yan kudi domin su tada rikici da hankulan mutane. A wannan karon akwai alamu kawunan matasa sun waye. Sun gane sun shiga kungiyoyin wanzar da zaman lafiya.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG