Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai zauna yau akan rikicin Syria


Taron kwamitin sulhu
Taron kwamitin sulhu

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD zai zauna yau da rana domin ya saurari bayanai dangane da halin da ake ciki a Syria, bayan da aka kwashe mako da barkewar sabuwar tarzoma, musamman a birnin Aleppo,birni na biyu a kasar.

Ana sa ran babban jami'in kula da harkokin siyasa na majalisar, Jeffrey Feltman shine zai yiwa kwamitin jawabi a wajajen rana yau Laraba.

Wannan mataki ya biyo bayan kudurin da kwamitin sulhun ya zartas jiya Talata,inda ya bukaci duka sassan da suke rikici, su kare asibitoci, da masu aikin kiwon lafiya, da cibiyoyin kiwon lafiya daga tarzoma, kuma za'a ladabtar ko aza laifi kan duk wanda yaki bin wannan umarni.

Matakin na kwamitin sulhu ya zama wajibi ganin munanan hare hare da ake kaiwa kan asibitoci a wurare da ake fama da fadace-fadace a fadin duniya.

A wasu hare hare da jiragen yakin Syria suka kaddamar har sau 30 ranar Asabar data wuce, a bangaren birnin Aleppo da yake hannun 'yan tawaye ya kashe akalla mutrane biyar. Wani roka da 'yan tawaye suka harba jiya Talata, ya farwa wani asibiti a Aleppon, ya kashe akalla mutane 3.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG