Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya Yace Tilas Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Su San Yadda Za Su Hana Fyade A Kwango


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban-Ki-moon, yace irin wannan fyade da aka yi a kasar Kwango ta Kinshasa ba abu ne da zai karbu ba, kuma tilas a hukumta wadanda suka aikata shi.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban-Ki-moon, yace irin wannan fyade da aka yi a kasar Kwango ta Kinshasa ba abu ne da zai karbu ba, kuma tilas a hukumta wadanda suka aikata shi.

A saboda munin fyaden da 'yan tawaye suka yi wa mata fiye da dari da hamsin a wani kauyen Kwango ta Kinshasa, Kwamitin Sulhun yace tilas sojojin kiyaye zaman lafiya su dauki matakan yin rigakafin wannan.

Kwamitin Sulhun -Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar da su dauki matakan hana abkuwar irin fyaden da aka yi wa mata masu yawa a kasar Kwango ta Kinshasa.

A bayan da ya saurari bayanai cikin sirri daga jami’an majalisar jiya alhamis, Kwamitin Sulhun yace har yanzu akwai abubuwan da ba a fahimce su ba a game da wadannan hare-hare da aka kai a kauyen Luvungi dake gabashin Kwango, da kuma irin martanin da sojojin kiyaye zaman lafiya dake yankin suka maida.

Sojojin kiyaye zaman lafiyar sun ce ba su samu labarin fyaden da aka yi wa mata su fiye da 150 ba sai bayan makonni biyu da abkuwar hakan, duk da cewa su na da sansani a kusa da kauyen na Luvungi.

Taswirar Lardunan Kivu ta Arewa da Kivu ta Kudu a gabashin Kwango ta Kinshasa inda ake ci gaba da rikici
Taswirar Lardunan Kivu ta Arewa da Kivu ta Kudu a gabashin Kwango ta Kinshasa inda ake ci gaba da rikici

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sojojin kiyaye zaman lafiya sun ziyarci kauyen a farkon watan Agusta lokacin da aka fara kai hare-haren, amma babu wanda ya fada musu abinda ke faruwa.

Shugaban Kwamitin Sulhun, jakada Vitaly Churkin na kasar Rasha, yace tilas sojojin kiyaye zaman lafiyar su kara daukan matakai na inganta sadarwa tsakaninsu da mutanen kauyukan da suke.

XS
SM
MD
LG