Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya Yayi Tur Da Hare-Haren Bam A Najeriya


Kura da hayaki daga tashin bam na biyu ranar jumma'a a Abuja.
Kura da hayaki daga tashin bam na biyu ranar jumma'a a Abuja.

Hukumomin tsaron Najeriya sun kama Raymond Dokpesi, manajan yakin neman zaben shugaban kasa na Ibrahim Babangida don yi masa tambayoyi game da hare-haren

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yayi tur da tagwayen hare-haren bam da aka kai ranar Jumma'a a Abuja, lokacin bukukuwan cikar shekaru hamsin da samnun 'yancin kan Najeriya, yana mai bayyana su a zaman babban laifi kuma maras hujja.

Kungiyar kare muradun yankin Niger Delta wadda ake kira MEND a takaice, ta dauki alhakin kai hare-haren wadanda suka kashe mutane 12. Wani tsohon shugaban kungiyar, Henry Okah, yana cikin mutane guda 9 da aka tsare dangane da hare-haren na bam.

An kama Okah ranar asabar a kasar Afirka ta Kudu inda yake da zama. Ya musanta cewa akwai hannunsa a wannan harin.

Haka kuma, hukumomin tsaro a Najeriya sun tsare domin yin tambayoyi ma babban darektan yakin neman zaben shugaban kasa na tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Ibrahim Babangida. Raymond Dokpesi shi ne mai gidan telebijin na AIT mai zaman kansa, wanda aka bayyana a zaman mafi girma a Najeriya. Shi ne kuma yake jagorancin kyamfe na Babangida wanda ke neman kawar da shugaba Goodluck Jonathan a zaben da aka shirya gudanarwa a watan Janairu.

Tsare Dokpesi da aka yi ya jefa ayar siyasa cikin binciken hare-haren bam din na ranar jumma'a.

Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana tababa a kan ko kungiyar MEND ce ta kai hare-haren, yana mai dora laifin harwe-haren a kan wata karamar kungiyar 'yan ta'adda wadda ke wajen Najeriya.

XS
SM
MD
LG