Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru a Jamhuriyar Niger sun dauki matakin yaki da cutar shan Inna


Wata mace tana jinyar yaronta a asibiti
Wata mace tana jinyar yaronta a asibiti

ADAPTER: Likitoci a Janhuriyar Niger suna nan suna fadi tashi da nufin kawar da cutar shan inna tsakanin kananan yara

Likitoci a Janhuriyar Niger suna nan suna fadi tashi da nufin kawar da cutar shan inna tsakanin kananan yara daga haihuwa zuwa ‘yan shekaru biyar da aihuwa, sama da dubu daya tare da kaddamar da wani shirin allurar rigakafi da likitocin ke kyautata zaton zai taimaka wajen shawo kan cutar.

A cikin hirarshi da wakilin Sashen Hausa Chaibou Mani, kwamishin lafiya na jihar Maradi Mahaman Lawali Manzo , ya yi kira ga iyaye su rungumi shirin su fito da ‘ya’yansu su sami rigakafin.

Kwamishinan ya fayyace muhimmancin allurar riga kafi da kuma dalilin da yasa gwamnati take kara kaimi wajen yaki da cutar, inda yace yaro daya dake dauke da cutar yana iya zama hadari ga kasar baki daya da makwabtan kasar harma da sauran kasashen duniy,a sabili da yadda cutar ke yaduwa kamar wutar daji.

Kwamishinan lafiyan yace an sami yaro guda daya dauke da cutar a kusan karshen shekarar da ta gabata a jihar Maradi, ya bayyana cewa kasancewa Niger na makwabta da daya daga cikin kasashe hudun da ake fama da cutar a duniya yasa yake zama da kalubala a iya shawo kan cutar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG