Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru Kan Sha'anin Tsaro da Shari'a Sun Yaba da Sako Fursunoni


Wadanda ake zargin cewa ‘Yan Kungiyar Boko Haram ne sun hada da Muhammad Nazeef Yunus, da Umar Musa, da Mustapha Yusuf, da Ismaila Abdulazeez, da kuma Ibrahim Isa.
Wadanda ake zargin cewa ‘Yan Kungiyar Boko Haram ne sun hada da Muhammad Nazeef Yunus, da Umar Musa, da Mustapha Yusuf, da Ismaila Abdulazeez, da kuma Ibrahim Isa.

Sai dai malamai irinsu Sheikh Bala Lau, sun ce akwai manyan malamai irinsu Sheikh Nazifi da aka yi musu sharri aka kama su, ana kuma tsare da su har yanzu

Kwararru kan harkokin tsaro da shari'a a Najeriya sun yaba da matakin da gwamnati ta dauka na sako fursunoni 167 daga cikin wadanda ake tsare da su da sunan Boko Haram, amma sun ce ya kamata a sako duk wadanda babu wata hujjar da za a iya kai su kotu da ita.

Wani kwararre kan sha'anin tsaro, kuma tsohon jami'in tsaro na farar kaya a Najeriya, Mr. Habu Dan Mallam, ya yaba da sakin mutanen yana mai cewa tun farko abinda ya kamata ayi ke nan. Yace a kasa kamar Najeriya mai ikirarin dimokuradiyya, tilas ne a gabatar da mutum a gaban kotu idan akwai hujjar tsare shi domin kotu ta yanke hukumci kan a sake ko a tsare shi, amma ba a yi ta tsare da shi na tsawon lokaci ba tare da wata tuhuma ba.

Shi ma masanin shari'a, Barrister Solomon Dalung, ya ce sakin mutanen mataki ne mai kyau, amma ya tambayi ko wace hujja ake da ita ta kin sakin wadannan mutane tun tuni? Yace akwai kamshin siyasa a cikin lamarin, amma dai wannan matakin farko ne mai alkhairi.

Shi ma shugaban kungiyar Izala ta Najeriya, Sheikh Bala Lau, ya yaba da sakin mutanen, amma yace cin zarafi ne yadda ake kame mutanen da ba su san baki ba, balle fari, har yayi misali da wani sanannen malami na addinin Islama a Jos, Malam Nazifi, wanda aka kama ana kuma tsare da shi ba tare da an gabatar da shi a kotu ba.

Sheikh Bala Lau yayi kiran da a gaggauta sakin Sheikh Nazifi da ire-irensa wadanda naka musu yarfe, ko kuma an san cewa akwai wata makarkashiya a game da kama su da aka yi.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG