Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Larabar Nan Sojojin Najeriya Zasu Fara Isa Kasar Mali.


Sojojin Faransa a Mali
Sojojin Faransa a Mali
Najeriya zata tura sojojinta zuwa Mali nan da sa’o’I 24, sannan daga bisani saura su biyo baya cikin mako. Wannan lamari yazo a lokacinda sojojin Faransa suke cigaba da fafatawa da mayakan sakai masu kishin Islama a arewacin kasar, yayinda ake dakon gudumawar sojoji daga kasashe dake yammacin Afirka.

A maraicen litinin ne shuga Goodluck Jonathan yace ckin makon nan sojojin Najeriya zasu isa Mali. Kakakin rundunar sojojin Najeriya Colonel Yerima Mohammed, ya gayawa Muriyar Amurka cewa, gobe laraba za a tura sojoji 190 watau kamfani daya, sannan daga bisani a tura 700.

A cikin ‘yan kwanakin nan, ‘yan tawayen kasar wadanda suka kama arewacin Mali, sun danna ta kudanci zuwa cikin yankuna dake hanun gwamnati. A karshen makon jiya Faransa ta tura jiragen yakinta da dakaru da suka shiga cikin rikicin, Faransa tana bayyana fargabar ‘yan tawayen suna iya afkawa Bamako, babban birnin kasar, saboda haka tilas a taka musu .

Tun cikin watannin baya ne kasashe dake yammacin Afirka suke shirye shiryen tura sojoji da karfinsu ya kai dubu uku zuwa Mali domin su taimaka wa gwamnatin ta kwace arewacin kasar daga hanun ‘yan tawaye. Shugaba Jonathan yace kwamandan da zai jagoranci sojojin Najeriya a Mali tuni ya isa kasar, tareda kwararru daga rundunar mayakan saman Najeriya.

Kungiyoyin mayakan sakai sun soki lamarin Faransa, sabo da tsoma hanu da ta yi cikin rikicin na Mali, su na masu cewa, rikicin zai kasance ga Faransa, kamar yadda Afghanistan ta zama ga kasashen yammacin duniya, musamman Amurka.

Frayin ministan Mali, Django Cissoko, ya kira kungiyoyin ‘yan tawayen a matsayin ‘yan ta’adda, da mabarnata.
XS
SM
MD
LG