Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Laurent Gbagbo a Shirye ya Ke a Tattauna Akan Rikicin Ivory Coast


Rikici na kara tsananta a ksar Ivory Coast tsakanin magoya bayan Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara
Rikici na kara tsananta a ksar Ivory Coast tsakanin magoya bayan Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara

Wani kakakin shugaban kasar Ivory Coast mai ci Laurent Gbagbo ya ce shugaban a shirye ya ke a canza miyau.

Wani kakakin shugaban kasar Ivory Coast mai ci, Laurent Gbagbo, ya fada cewa shugaban wanda ruwan rikici ya ciwo a shirye ya ke a tattauna don a warware rikicin siyasar kasar da ke tsananta.

Laurent Gbagbo a Shirye ya Ke a Tattauna Akan Rikicin Ivory Coast
Laurent Gbagbo a Shirye ya Ke a Tattauna Akan Rikicin Ivory Coast

Kakaki Ahoua Don Mello ya gayawa gidan Rediyon Muryar Amurka a yau Jumma'a cewa akwai wata dama ta zahiri ta iya yin irin wannan tattaunawa, bayan da Kungiyar Kasashen Afirka ta bayar da shawarar cewa a shimfida sharudan yin tattaunawar.

Mr.Gbagbo na ci gaba da kalubalantar kiraye-kirayen da kasashe ke yi cewa ya mika mulki ga abokin jayayyar shi Alassane Ouattara wanda Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Afirka su ka amince da shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar na watan Nuwamba.

A halin da ake ciki kuma, Majalisar Dinnkin Duniya ta ce duk wani harin da sojojin da ke yin biyayya ga Gbagbo su ka kai da manyan makaman igua, na iya zama wani mugun laifin cutawa bil Adama.

Sojojin sun kaddamar da hari a birnin Abidjan, cibiyar hada-hadar kasuwancin kasar Ivory Coast su ka halaka mutane ishirin da biyar a kalla a unguwar Abobo wadda ke da yawan magoya bayan Ouattara.

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana kaduwar shi game da kashe-kashen sannan ya bukaci Kwamitin Sulhun Majalisar da ta kara daukan matakai akan wadanda su ka shirya wannan tashin hankali.

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya na bayyana kaduwar shi akan kashe-kashen unguwar Abobo.
Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya na bayyana kaduwar shi akan kashe-kashen unguwar Abobo.

Kakakin na shugaba Gbagbo ya musanta cewa sojojin gwamnati ne su ka kai harin na ranar alhamis, ya ce sojojin gwamnati ba sa ma unguwar Abobo lokacin da harin ya wakana.

XS
SM
MD
LG