Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyoyin Gwamnatin Tarayya Sun Fantsama cikin Yajin Aiki


'Ya'yan kungiyar lauyoyin Najeriya.
'Ya'yan kungiyar lauyoyin Najeriya.

Yayin da alkalan kotuna ke yajin aiki sai gashi lauyoyin gwamnatin tarayya su ma sun fantsama ciki.

Mai magana da yawun lauyoyin yace yajin aikin na gargadi ya zama wajibi domin kunnen kashi da gwamnatin ta dinga yi har na shekaru ashirin da daya akan lamuransu.

Shekaru ashirin da daya da ta gabata gwamnatin tarayya ta bada umurni cewa gwamnatocin jihohi su kyautata albashin lauyoyinsu tare da hakinsu. Jihohi da dama sun yi to saidai abun mamaki ita gwamnatin tarayya da ta bada umurnin bata tabuka komi ba.

Tunda sun jira tayi wani abu bata yi ba shi ya sa suka dauki shawara fantsama cikin yajin aiki. Malaman jami'a da likitoci duk sun yi yajin aiki kafin a sauraresu.Tunda ma kotuna na yajin aiki to kamata yayi su ma su shiga domin su san abun da gwamnati zata yi.

Duk cikin lauyoyin gwamnati kama daga jiha zuwa gwamnatin tarayya lauyoyin tarayya su ne suke karbar albashi mafi kankanta. A jihar Imo misali lauyan gwamnati a mataki na tara na karbar nera dubu dari uku wata. Amma a gwamnatin tarayya lauyan gwamnatin tarayya dubu hamsin yake karba wata.

Yanzu dai kura ta kai bango domin lauyoyin sun sha rubutawa shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya da shugaban majalisar datttawa amma duk shiru kamar an shuka dusa.

Ga rahoton Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG