Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebola Ta Kashe Mutum na Uku A Najeriya


Likitoci a Jihar Legas, sun gudanar da taron manema labarai domin tattauna batun cutar zazzabin Ebola, musamman ma biyo bayan mutuwar mutum na uku daga cutar a birnin Ikko.

Likitocin sun kira wannan taro ne domin fadakar da sauran ma’aikatan asibiti dangane da cutar ta Ebola, saboda sune suke fara karo da masu cutar, lamarin da ka iya kaisu ga daukar cutar.

Amma likitocin sun koka akan cewa gwamnati bata yi tanadin wadatattun kayan kariya ba daga wannan cuta.

Daya daga cikin likitocin yace “bamu yarda ba, ko kadan na cewa an dauki hanyar kare mu, mu ma’aikatan asibiti, daga wannan cuta, saboda haka muke rokon gwamnati tayi abunda ya kamata.

Yanzu haka dai an kwashe makonni shida, likitoci a duk fadin tarayyar Najeriya suna cikin yajin aikin sai baba ta gani, biyo bayan rashin jituwa da suka samu da gwamnatin Tarayya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG