Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Macizai da Namundaji na Kahse 'Yan Gudun Hijira a Adamawa


Wasu 'yan gudun hijira.
Wasu 'yan gudun hijira.

Wadanda suke gudun hijira sanadiyar harin 'yan Boko Haram a jihar Adamawa sun fada cikin wahala. 'Yan Boko Haram sun killayesu yadda babu hanyar kai masu doki.

Mutanen sun tagayyara sabili da rashin abinci, magani da ma wurin sa kai kama daga yankin Madagali zuwa Michika.

Rahotanni na nuwa cewa akwai 'yan gudun hijiran da suka rasa rayukansu sakamakon rashin abinci da cizon macizai da wasu namundaji.

Shugaban karamar hukumar Michika ya bayyana irin halin da mutanensa suka shiga. Wadanda suke kan duwatsu dabobin daji na kashesu. Suna fama da yunwa da rashin magani. Ya kira gwamnatocin jiha da tarayya da ma kungiyoyin kasashen duniya su taimakesu. Babbar bukatarsa ita ce mutanensa su samu su koma gidajensu. A taimaka masu da abinci da duk abunbuwan rayuwa na yau da kullum.

Shi ma shugaban karamar hukumar Madagali Mr James Watanda yace sakamakon kawanyar da 'yan Boko Haram suka yi a yankinsa ya kasa dauko mahaifiyarsa mai kimanin shekaru tamanin da biyar sabili da rashin hanya. Ko zuwa kan tsaunukan babu hanya domin 'yan Boko Haram sun toshe koina da ina.

Ita gwamnatin jihar Adamawa ta bakin kakakinta Mr. Peter Elisha tace zasu kara neman taimako domin abun ya fi karfin gwamnatin jihar. Abun da jihar ke samu bai isa ta dauki irin wannan nauyin ba. Kakakin ya kira masu hannu da shuni irin su Aliko Dangote su yi taimako.

'Yan Boko Haram din sun tarwatsa kimanin mutane dubu goma a yankin tsakanin Madagali da Michika.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG