Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun Adawa Na Ghana Yace Yanada Karfin Gwuiwar Samun Nasara


Nana Akufo-Addo, madugun 'yan adawa a Ghana najam'iyyar NPP
Nana Akufo-Addo, madugun 'yan adawa a Ghana najam'iyyar NPP

A Ghana,madugun 'yan hamayya a zaben kasar Nana Akufo-Addo, yace yana da kwarin guiwar zai yi nasara, duk da haka yayi kira ga magoya bayansa su baiwa hukumar zaben kasar sarari ta gudanar da aikinta.

Dan takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar NPP, yayi magana ga magoya bayansa a birnin Accra jiya Alhamis, a dai dai lokcinda hukumar zaben kasar ta fara sakin sakamkon zaben sannu a hankali daga zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa da aka yi ranar Laraba.

Babbar jam'iyyar hamayyar ta NPP tace bisa la'akari da alkaluman bayanai da ta tara na sakamakon zaben ya nuna cewa dan takararta Nana Akufo Addo ne ya lashe zaben. Haka nan wasu 'yan takara su biyar suma sun goyi bayan alkaluman da suka nuna Nana Akufo ne ya sami nasara. Amma har yanzu shugaban kasar John Mahama da jam'iyyarsa ta NDC mai mulkin kasar bata ayyana cewa ta sha kaye ba.

Magoya bayan madugun adawa Nana Akufo Addo na shirin yin biki
Magoya bayan madugun adawa Nana Akufo Addo na shirin yin biki

Hukumar zaben kasar tace ta hakikance an yi katsalandan da sakamkon zaben da ake turo mata da kafofin sadarwa na zamani, saboda haka ne take jinkirta bayyana sakamakon zabe har sai ta karbi sakamakon zabe a rubuce kan takarda.

An zafafa yiwa hukumar kiraye kiraye ta kafofin sada zumunta cewa ta hanzarta bayyana sakamakon zaben. Akufo Addo yayi kira ga magoya bayansa su kai zuciya nesa.

XS
SM
MD
LG