Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai doki ya koma kutiri a majalisa inji Hunkuyi


Ranar da aka rantsar da Abubakar Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa a Najeriya
Ranar da aka rantsar da Abubakar Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa a Najeriya

Sulaiman Usman Hunkuyi na daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a Najeriya musamman a siyasar Kaduna. Inda yake ganin an dauki dusar baki an bawa akuyar baki ne game da abinda ke faruwa a Majalisun Tarayyar Najria.

Abokin aikinmu Sahabo Imam Aliyu ya tattauna da Sulaiman Usman Hunkuyi tsohon dan takarar gwamnan jihara Kaduna, game da badakalar da ke kai kawo a Majalisar Dajjawan Najeriya. Ya tabbatarwa da Muryar Amurka cewa in ha rana son bin doka shine sai an hada da kai kara kotu.

Ya bayyana cewa an cutar da mutanen Najeriya game da yadda aka raba mulkin gida biyu aka bawa jam’iyyar PDP da ba ita ke da mulki ba. A ganinsa an yi zaben da aka yi bai kaya ba wajen fidda Abubakar Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu.

Hunkuyi yace mai doki ya koma kuturi ne. Wancan karon na gwamnatin da ta shude in ba a manta ba, yace Tambuwal da mataimakinsa gaba daya ‘yan jam’iyyar PDP ne. Tsohon dan takarar gwamnan Kadunan yace dalilin siyasa shine yin zabe ba kawai a yiwa al’amari hawan kawar ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

XS
SM
MD
LG