Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai shan maganin kanjamau yana bukatar hadin kan iyali da kuma al’umma - Dr.Dankyau


Dr. Musa Dankyau na jami'ar Bingham, Nigeria
Dr. Musa Dankyau na jami'ar Bingham, Nigeria

Kwararru sun ce mai shan maganin cutar kanjamau yana bukatar hadin kai da goyon bayan iyali

Shugaban Sashen horas da aikin magani da kuma jinya na jami’ar Bingham a Najeriya Dr. Musa Dankyau ya bayyana cewa, mai shan maganin cutar kanjamau yana bukatar hadin kai da goyon bayan iyali da kuma al’umma domin ganin maganin ya yi aiki yadda ya kamata.

Likitan ya kuma bayyana cewa, daya daga cikin dalilan da ya sa maganin rage kaifin cutar kanjamau baya aiki shine, yawancin lokuta masu jinya basu sanar da iyalansu halin da suke ciki, ta dalilin haka iyalan basu san ko suna dauke da cutar ba balle suma su nemi magani.

Dangane kuma da ikirarin da wadansu likitoci ko masu maganin gargadiya suke yi na iwa warkar da cutar kanjamu, Dr. Musa Dankyau yace kawo yanzu, babu wani binciken da aka gudanar da ya tantance wadannan harsashe.

Likitan ya kuma bayyana cewa, cin kayan lambu da kuma ganye yana taimakawa wajen gina jiki, amma ba maganin cutar kanjamau ba.

Dr. Musa Dankyau ya bayyana haka ne a cikin hirarsu da Grace Alheri Abdu yayin taron yaki da cutar kanjamau na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Washington DC.

Hira Da Dr. Musa Dankyau

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG