Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kudurin da Zai Kaucewa Kuncin Kudi


Husumiyar majalisar dokokin Amurka.
Husumiyar majalisar dokokin Amurka.
Majalisar dattawan Amurka ta amince da shirin da zai kauce wa siradin kasafin kudi, wanda zai yi karin haraji da rage kudaden da gwamnati ke kashewa bayan da aka share kwana biyu ana muhawara, da neman daidaituwa tsakanin fadar shugaban kasa ta White House, da ‘yan majalisar dokokin na jam’iyyar Republican.

A kuri’ar da aka jefa a safiyar yau Talata, majalisar dattawa ta amince da shirin da kuri’a 89 na yarda, da kuri’a 8 na rashin amincewa.

Shugaba Barack Obama ya jin-jina wa majalisar dattawan, kuma yayi kira ga majalisar wakilai da ta amince da wannan shiri ba tare da bata lokaci ba. ‘Yan majalisar wakilan na shirin haduwa yau da rana, domin fuskantar wannan shiri.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa Mitch McConnel yace daidaituwan da aka samu, wanda zai hana karin haraji ga yawancin Amurkawa, ba yadda ake so bane. Ya kuma gode wa mataimakin shugaban kasa Joe Biden, wanda yayi aiki da shuwagabanni a majalisar dattawan domin cimma wannan daidaituwa.

A karkashin shirin, mutanen da ke samun sama da dala dubu 400 , da iyalai masu samun sama da dala dubu 450 a shekara, zasu ga karin haraji. Sannan kuma shirin ya kara watanni biyu kafin ayi tanadin yadda za’a rage kudaden da ake kashewa a harkokin tsaro, da shirye-shiryen cikin gida, wanda zai jawo cece-ku-ce tsakanin jam’iyyun guda biyu.
XS
SM
MD
LG