Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Aza Takunkumi Ga Laurent Gbagbo da Gwamnatinsa

Majalisar kare hakkin bil'adama ta majalisar dinkin Duniya.
Majalisar kare hakkin bil'adama ta majalisar dinkin Duniya.

Dakaru dake adawa da shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo,sun kama birnin Yamoussoukro,birni da a hukumance shine babban birnin kasar,kodashike sojoji dake biyayya ga Gbagbo, suke da iko kan cibiyar Gwamnati dake Abidjan.

Wata kakakin rundunar ‘yan tawaye dake biyayya ga Mr. Ouattara, ta gayawa sashen Faransa na MA, cewa jiya Laraba ce sojojin suka shiga birnin Yamoussoukro,bayan sun sami nasarori a kutse da suka yi a fadin kasar. Mazauna birnin sunce sojoji dake biyayya ga Gbagbo sun tsere,yayinda sojojin Ouattara ne suke tattakawa ta cikinkafa da kuma motoci kan titunan birnin.

Haka kuma kakakin tace ‘yan tawaye sun kama birnin San Pedro dake kan gabar teku.Mazauna birnin sunce ‘yan tawaye sun shiga birnin kuma suna jin karar bindiga.

A wani ci gaba kuma,jiya laraba kwamitin sulhu na MDD ya aza takunkumi kan Mr. Gbagbo saboda yaki ya mika mulki,bayanda an ayyana Mr.Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi cikin watan Nuwamba.Takunkumin ya hada da na tafiye tafiye da kuma akan kadarorin Mr.Gbagbo,matarsa,da wasu hadimai uku.

XS
SM
MD
LG