Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta Ce An Kashe Fararen Hula da Yara a Afirka ta Tsakiya


Bangui, Afirka ta Tsakiya, Dec. 5, 2013.
Bangui, Afirka ta Tsakiya, Dec. 5, 2013.

A Afirka Ta Tsakiya wasu 'yan bindiga sun kashe mutane goma sha biyu da suka hada da yara.

Majalisar Dinkin Duniya tace wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe a kalla farin kaya goma sha biyu da suka hada da kananan yara, a Damokaradiyar Afrika ta tsakiya inda harkokin tsaro suke kara tabarbarcewa tun bayan juyin mulkin da aka gudanar a watan Maris.

Tashin hankalin ya barke yayinda kwamitin sulhu yake shirin kada kuri'a yau alhamis na tura karin dakarun Faransa zuwa kasar domin taimakwa wajen maido da doka da oda.

Majalisar Dinkin Duniya tace an kai harin ne ranar Litinin a wata al'umma dake tazarar kilomita casa'in dake arewa maso gabashin Bangui babban birnin kasar.

Amy Martin shugaban cibiyar ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya dake bangui yace akwai alamun cewa, mayakan Kirista da ake kira anti-balaka suna kai hare hare kan makiyaya Musulmi. A cikin sanarwar, tace, wannan na daga cikin tashe tashen hankali da aka fuskanta a baya bayan nan.

Faransa ta fara kokarin kara yawan dakarunta a jamhuriyar Afrika ta tsakiya da zuwa kimanin dubu daya.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG