Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq, ya gaya ma manema labarai a birnin New York cewa ba da wasa ba MDD ke daukar zargin cewa dakarun kiyaye zaman lafiyar ba su taimaki farar hula ba a lokacin bukata ba, ya kara da cewa kwamandan MDD a Sudan Ta Kudu na nazarin al'amarin.
Kafar jaridar Associated Press ta ruwaito shaidun gani da ido da shugabannin jama'a na cewa sojojin gwamnatin Sudan Ta Kudu sun yi fade ma mata da 'yan matan Nuer da dama a makon jiya daura da rukunin gidajen MDD, inda su ka nemi mafaka daga fadace-fadacen baya-bayan nan da aka yi a babban birnin kasar.