Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa akan tarzomar Nigeria.


Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana damuwa akan tarzomar kabilanci data addini da suke faruwa a tsakiyar Nigeria, inda kwanaki aka kashe wani mutum da yayansa bakwai

Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana damuwa akan tarzomar kabilanci data addini da suke faruwa a tsakiyar Nigeria, inda kwanaki aka kashe wani mutum da yayansa bakwai. Wani mai magana da yawun hukumar kare hakkin jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya Rupert Colville yace fafatawa da ake yi a yankin da ake cewa Middle Belt tun watan Augusta sun kashe kimamin mutane saba’in.

A wata sanarwar daya gabatar jiya juma’a Mr Rupert Colvile yayi kira ga hukumomin Nigeria da su dauki matakan umul’abaisin iri wadannan rikice rikice musamma ma tsakanin matasan Musulmi da Kirista a jihar Plato.

Haka kuma Mr Colvile yace ya kamata suma jami’an tsaro su san irin matakan da zasu dauka dangane da barkewar irin wadannan tarzomar domin kaucewa kara rinchabewar al’ummar.

XS
SM
MD
LG