Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Za Ta Kori Dakarun Da Suka Ci Zarafin Mata Da Yara


Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon
Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon

Majalisar Dinkin Duniya ta kuduri aniyar hukunta duk wanda aka samu da laifin cin zarafin yara da mata da sunan kwantar da tarzoma.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya amince da korar duk wani wanda aka samu da hannu cikin zargin aikata cin zarafin saduwa a lokacin da sojoji ke ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasashen duniya.

Bangaren Majalisar sulhu na MDD ya zabi rungumar kundin hukunta laifuffukan da Amurka ta fitar a matsayin a matsayin na wucin gadin da za a iya bitarsa don yin gyara sannan a yi amfani da shi don yin hukunci.

Jakadar AMurka a MDD Samantha Power ta kara da cewa, “Wannan mataki ya nuna a fili cewa aikinmu mu dau matakin da ya dace ga duk wanda aka samu da laifin cin zarafin mata da yara da sunan kiyaye zaman lafiya.

Shima jakadan Birtaniya a MDD cewa yayi, wannan magana ce ta gaggauta daukar matakin da ya dace akan wannan babban zargin laifi na cin zarafi ta inda bai kamata ya bullo ba.

XS
SM
MD
LG