Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya za ta yi taro game da tsokanar Korea ta Arewa


Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un na Il
Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un na Il

Magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-moon ya yi kira ga gwamnatin Pyongyang data dakatar da wadannan gwaje-gwajen tsokanar da take yin a makamai masu linzami.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na shirin taro a ranar Juma’a mai zuwa don tattauna maganar Korea ta Arewa game da sake gwada harba makaman Roka samfurin Ballistic masu cin gajeren zango.

Kakakin Ban Ki-moon Stephane Dujjaric yace, matsayin da ake ciki na gwaje-gwajen Korea ta Arewa a zirin iyakokin Korea yana da matukar sosa zukata. Saboda haka suna kira ga Pyangyong yin da’a ga dokokin kasa da kasa.

Korea ta Arewa ta hahharba makamanta masu linzami da sunan gwaji, wanda hakan ya sabawa dokar Majalisar Dinkin Duniya, na haramta mata mallakar makaman Nukiliya.

Jami’an gwamantin kasar sun ce Rokar tasu ta ci nisan Kilomita 800 kafin ta tunjima cikin gabashin teku da ke arewaci.

XS
SM
MD
LG