Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Jamus Ta Amince Turkiya Ta Yiwa Aminiyawa Kisan Kare Dangi


Majalisar Dokokin Jamus yayinda da take kada kuri'a a kan kudurin da ya amince Turkiya ta yiwa aminiyawa kisan kare dangi lokacin yakin duniya na daya a shekarar 1915
Majalisar Dokokin Jamus yayinda da take kada kuri'a a kan kudurin da ya amince Turkiya ta yiwa aminiyawa kisan kare dangi lokacin yakin duniya na daya a shekarar 1915

A Jamus, wakilan majalisar dokokin kasar da gagarumar rinjaye, sun amince da kudurin da ya ayyana kisan aminiyawa a zamanin yakin duniya na daya, a hanun dakarun Turkiyya, a zaman kisan kare dangi.

"Kudurin da majalisar dokokin Jamus, ta amince da shi, zai yi illa ga dangantaka tsakanin Jamus da Turkiya," inji shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdgan, jim kadan bayan da majalisar ta kada wannan kuri'a.

Yayi magana ne a lokacin wani taron da manema labarai a Nairobi babban birnin kasar Kenya, Erdogan,yace bayan da kasar ta bukaci jakadar kasar a Jamus ya koma gida domin tattaunawa, kasar daga bisani zata duba matakai da zata dauka gaba, a zaman martani kan wannan kuduri.

Ma'aikatar harkokin wajen Turkiya ta gayyaci karamin jakadan Jamus zuwa helkwatarta bayan da majalisar dokokin Jamus ta amince da wannan kuduri.

Shugabar Jamus Angela Merkel, tace kasashen biyu suna kyakkyawar dangantaka mai zurfi, duk da banbance-banbance dake akwai kan wani batu guda daya tilo."

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG