Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Yi Dokar Hana Cin Zarafin Mata


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Majalisar Dokokin Najeriya ta zartas da dokar hana cin zarafi ko musgunawa ko tsangwamar 'ya'ya mata tun daga makarantun Firamare zuwa Jami'a tare da sa hukunci mai tsanani.

Duk malamin da aka kama kuma aka tabbatar da laifin muzgunawa ko tsangwama ko batanci da lalata ‘ya mace daga makarantar Firamare har zuwa Jami’a to zai tafi gidan Yari har tsawon shekaru biyar ko kuma ya biya tarar Naira Miliyan Biyar.

Wannan shine hukuncin dake kunshe a dokar hana muzgunawa ‘ya ‘ya mata da Majalisar Dokokin Najeriya ta Zartar. Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, yana daga cikin ‘yan Majalisar Dattawa da suka yi aikin wannan doka, yace cin zarafin da ake yiwa ‘ya ‘ya mata yasa suka duba lamarin suka kuma yi doka akanta. Ya ci gaba da bayanin cewa idan kuma aka samu wata mace da yin kazafin karya cewa wani malami ya ci zarafinta, aka bincike aka tabbatar da cewa tayi karya to za koreta daga makaranta baki daya.

Gloria Laraba Shoda, shugabar gamayyar kungiyoyin mata ta kasa tace ta ji dadi matuka da wannan mataki da Majalisar Dattawa suka dauka, domin an dade ana irin wannan rashin ‘da’a a makarantu. Da kuma yi fatan cewa dokar zata yi tasiri, domin wasu lokuta akan cin hanci da rashawa kan dakile dokokin irin wannan.

Wannan mataki da Majalisar ta dauka yazo dai dai da kamfen din da mahukuntan kasar suka kaddamar na hana azabtar da yara ko cin zarafinsu, wanda a halin yanzu jihohi 23 cikin 36 da birnin Tarayya Abuja ne suka rattaba hannu a dokar ta kare hakkin yara.

Domin karin bayani ga rahotan Madina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

XS
SM
MD
LG