Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makahon Malamin Masar Ya Mutu A Fursunan Amurka


Marigayi Sheikh Omar Abdel-Rahman
Marigayi Sheikh Omar Abdel-Rahman

Jami’an gidajen yarin Amurka sun bada sanarwa mutuwar wani Shaihin Malamin addinin Islama dan asalin kasar Masar, wanda aka daure sakamakon kamashi da hannu a kokarin tarwatsa surorin tarihi na birnin New York anan Amurka.

Jami’an gidan Fursuna da ke Butner a Carolina ta Arewa ne suka tabbatar da mutuwar tasa a yau Asabar. Inda suka ce Sheikh Omar Abdel-Rahman yam utu ne da sanyin safiyar yau bayan ya sha fama da jiyar cutar Sikari da kuma mai nasaba da ciwon zuciya.

Malamin na daya daga wadanda aka alakanta da harin da aka taba kaiwa cibiyar kasuwanci ta World Trade Center a 1993, wanda kuma tun 1995 ake tsare da shi sakamakon kokarin shirya tarwatsa tubalolin tarihin Manhattan ciki har da Majalisar Dinkin Duniya.

Da kuma kokarin tarwatsa katafariyar gadar Manhattan da ma wasu hanyoyin karkashin kasar da suke mahada ne ta shige da ficen motoci zuwa cikin birnin. Bisa abinda ya bayyana cewa kokari ne na dakile taimakon da Amurka ke bawa Isra’ila da Misira. Sannan duk da shafe sama da shekaru 20 a Fursunan Amurka har yanzu yana da mabiya.

Shekarun Abdel Rahman 78 wanda ake wa lakabi da da Blind Sheikh a Turance, wato Makahon Malami. Da yake ya rasa idanunsa tun yana dan karamin yaro sakamakon ciwon sukari. Dan Marigayin ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labaran Reuters cewa jami’an Amurka sun sanar da su mutuwar baban nasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG