Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Makaranta Fiye Da Dari Uku Gwamnatin Neja Ta Dakatar


Gwamnan Neja Dr. Babangida Aliyu shi ne a tsakiya
Gwamnan Neja Dr. Babangida Aliyu shi ne a tsakiya

Kimanin malaman makarantun sakandari dari uku da talatin da biyu gwamnatin jihar Neja ta dakatar ko ta kora gaba daya daga bakin aiki.

A wani yunkuri na tabbatar da inganta karatu a makarantun gaba da firamare a jihar Neja gwamnati ta yi tankade da rairayar malamanta lamarin da ya yi sanadiyar kakkabe malamai fiye da dari uku.

Gwamnatin jihar ta dauki matakan ne sabo da dalilai da dama da suka hada da rashin ilimin da ya kamata su kama irin wannan aikin da kuma kin zuwa wurin aiki. Alhaji Uba Hassan Kuta shi ne shugaban bada ilimi bai daya na jihar ya ce daga cikin malaman da aka dakatar har da wasu guda talatin da bakwai da aka samu da matsalar kamuwa da cutar haukacewa. Wadannan da suka samu tabin hankali jami'in ya ce za'a zauna a tantance a gano abun da ya sa suka samu tabin hankali da kuma lokacin da abun ya samesu. Ya ce idan sun dade da aiki sai ayi masu ritaya.

Gwamnatin ta bada sanarwa cewa yanzu haka an fara daukar sabbin malamai domin maye gurbin malaman da aka dakatar. Haka kuma za'a kara malamai a waje-jen karkara. Ya kara da cewa a tantancen da suka yi akwai masu aiki a ofishin ma'aikatar ilimi da suke da ilimin koyaswa da basa son a kirasu malaman makaranta. Irin wadannan za'a mayar dasu aji su koyas da yara.

A wani hali kuma na kulawa da ilimin yara mata gwamnatin jihar da hukumar kula da harkokin yara da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya sun sa hannu a kan yarjejeniyar daukar nauyin yara mata 120 da ilimin gaba da sakandare . Wannan wata dama ce game da samar ma 'ya'ya mata ilimi.

Ga karin bayani
Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG