Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Hafsoshin Sojan ECOWAS Sun Tattauna Batun Kawar Da Laurent Gbagbo


Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da shugaba Boni Yayi na Jamhuriyar Benin su na tattaunawa lokacin taron kolin da ECOWAS ta yi kan rikicin siyasar Ivory Coast
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da shugaba Boni Yayi na Jamhuriyar Benin su na tattaunawa lokacin taron kolin da ECOWAS ta yi kan rikicin siyasar Ivory Coast

Wani jami'in sojan Najeriya yace kungiyar ta tatauna yadda za a yi amfani da karfi wajen kawar da Gbagbo idan ya ki sauka cikin lumana.

Wani jami'in soja na Najeriya, yace kungiyar kasashen yankin Afirka ta Yamma ta tattauna yin amfani da karfi wajen kawar da Laurent Gbagbo daga kan gadon mulkin kasar Ivory Coast, idan har ya ki sauka daga kan shugabancin cikin lumana ta hanyar shawarwari.

Kanar Mohammed Yerima ya fada yau jumma'a cewa manyan hafsoshin tsaro daga Kungiyar Tarayyar tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO a takaice, sun gana inda suka nazarci wani shiri na kawar da Mr. Gbagbo.

Amma kuma bai ce an tsaida lokaci na kai farmaki ba, yana mai fadin cewa za su sake ganawa a tsakiyar watan Janairu domin kammala tsara wannan shiri na kifar da Gbagbo.

Mr. Gbagbo dai ya ki sauka ya mika mulki ga baokin hamayyarsa, Alassane Ouattara, mutumin da duniya ta amince da cewa shi ne ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka gudanar a watan Nuwamba. Mr. Gbagbo yana gardamar sakamakon zaben.

Tun a farkon wannan makon, shugabannin Afirka ta Yamma sun mikawa Mr. Gbagbo takardar wa'adin dake cewa yana iya sauka cikin lumana a ba shi mafaka, ko kuma ana iya cire shi karfi da yaji. Ana sa ran wata tawagar ta ECOWAS zata sake komawa kasar Ivory Coast a ranar litinin domin ci gaba da tattaunawa.

Sakataren hulda da kasashen waje na Britaniya, William Hague, ya fadawa BBC yau jumma'a cewa Britaniya zata goyi bayan a tura rundunar sojojin da zata kawar da Mr. Gbagbo daga kan mulki idan aka kasa yin hakan ta hanyar tattaunawa, muddin dai Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wannan runduna.

XS
SM
MD
LG