Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Jami'an Tsaro da 'Yan Majalisar Dattawa Sun Yi Kiki da Kiki


Jami'an tsaro suke sintiri a birnin Maiduguri.
Jami'an tsaro suke sintiri a birnin Maiduguri.

'Yan majalisar dattawa da manyan jami'an tsaro sun yi wani taro na fiye da sa'o'i biyar inda suka tada jijiyoyin wuya kowanensu cikin bacin rai sabili da yanayin da kasar ke ciki.

An yi musayar yawu da tada jijiyoyin wuya yayn da manyan shugabannin tsaro da 'yan majalisar dattawa suka gana a asirce na fiye da sa'o'i biyar.

Labarai dake fitowa daga taron sun nuna cewa tabarbarewar tsaro da sabunta dokar ta baci su ne batutuwan dake kan gaba. Sanato Aliyu Ndume dan jihar Borno ne. Ya kuma bayyana dalilin da ya sa aka gayyacesu. Ya ce an kirasu ne su bayyana inda suka tsaya cikin aikin da suke yi karkashin dokar ta baci a jihohin da lamarin ya shafa. Ya ce suna son su gaya masu tsakaninsu da Allah ina aka tsaya domin mutane na ganin kamar kwaliya bata biya kudin sabulu ba. Dalili ke nan da ya sa suka dauki lokaci domin shugaban majalisar ya ce dole kowa ya fadi abun dake ransa. An bukaci su jami'an tsaron su bayyana damuwarsu idan akwai.Tun da an zo karshen shekara majalisar na iya taimaka masu su cimma burinsu domin a shawo kan tabarbarewar tsaro.

Sabili da dalilai na tsaro Sanato Ndume ya ki ya bayyana wa manema labarai matsalolin da jami'an tsaro ke fuskanta. Amma ya ce duk matsalolin sun shafi kowa da kowa, wato talaka da jami'an tsaro da 'yan majalisu da shugabannin gwamnati da ma masu zaman kansu.

Majalisar ta gamsu da wasu abubuwan da aka bayyana mata amma kuma akwai wasu da bata gamsu da su ba. Su jami'an tsaron an nuna masu abubuwan da ya kamata su yi da basu yi ba.Irin wannan tattaunawar yana gani zata taimaka. Da ana yin irinta tun farko da watakila an shawo kan lamarin tuntuni.

Babbar matsalar da ake fama da ita iatce zaman dar-dar da ake yi. Wannan lamarin bashi da nasaba da addini ko kabilanci. Da an cire zaman dar-dar da ya taimaka da yawa a cimma bukatar da ake so. Jami'an tsaro suna son a kawo karshen tashin tashina da ake ciki ko yau ma domin kowa ya koma cikin zaman lafiya da walwala. Jami'an tsaro sun ce ba gudu ba ja da baya sai sun cimma burin kawo zaman lafiya.

Medina Dauda nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:34 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG