Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kasashen Duniya Sun Damu da Rashin Tsaro a Najeriya - Shugaba Buhari


Shugaba Buhari da Shugaba Obama
Shugaba Buhari da Shugaba Obama

A firar da abokin aiki Sahabo yayi da shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari sun tabo abubuwan da suke da alaka da lamuran Najeriya

Jami'an gwamnatin Buhari sun tabbatar cewa akwa muhimman abubuwa uku da shugaban zai tattauna akansu da shugabanAmurka,

Akan wadannan da aka tambayi shugaba Buhari sai yace yana son mutane su gane cewa akwai manyan kasashe bakwai na duniya da ake kira G7. Su suka kirashi zuwa wurin taronsu a Jamus. Sun nuna damuwarsu akan rashin tsaro a Najeriya musamman a arewa maso gabas..Kasashen sun yialkawarin zasu taimaka.

Da shugaban ya koma Najeriya yayi kokarin rubutawa kasashen abubuwan da ake bukata da irin barnar da 'yan Boko Haram suka yi na kona makarantu da asibitoci da karya gadoji da makamantansu. Najeriya da kasashen dake makwaftaka da ita zasu hada gwiwa da bada sojoji domin yakar Boko Haram. Karshen wannan watan sojojin zasu fara aiki. Yanzu dai ana tara masu kayan aiki. Wadannan bukatun za'a aikawa manyan kasashen guda bakwai. Shugaba Buhari ya taho Amurka da wasikar shugaba Obama da ta kunshi bukatun.

Akan magance ta'adanci an tambayi shugaban idan Amurka zata iya taimakawa a kawo karshen ta'adancin ganin cewa bata iya yin haka ba a Afghanistan da Iraqi.Shugaba Buhari yace abun da ya faru a Afghanistan ba iri daya ba ne da na Najeriya. Taimakon da Amurka zata bayar shi ne ta koyas da sojojin Najeriya.

Ga karin bayani.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG