Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kasashen Duniya Sunce Tilas Gadhafi Ya Sauka


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton take jawabi a taron kasa da kasa da aka yi London dangane da kasar Libya.
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton take jawabi a taron kasa da kasa da aka yi London dangane da kasar Libya.

Shugabannin manyan kasashen duniya 40 da ke taro a London sun amince jiya Talata cewa dole fa ne Shugaban Libiya Muammar Gaddafi ya sauka, a daidai lokacin da su ka zurfafa tattaunawar da su ke yi da dakarun ‘yan tawaye

Shugabannin manyan kasashen duniya 40 da ke taro a London sun amince jiya Talata cewa dole fa Shugaban Libiya Muammar Gaddafi ya sauka, a daidai lokacin da su ka zurfafa tattaunawar da su ke yi da dakarun ‘yan tawaye kan yadda za a sauya tsarin gwamnati a wannan kasar wacce take arewacin Afirka.

Kodayake ba a zayyana batun canza gwamnati a kudurin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya da ya wajabta amfani da karfin soji kan dakarun gwamnatin Libiya ba, kasashe da dama sun yi amanna cewa Mr. Gaddafi ya rasa huruminsa don haka kamata ya yi ya mika ragamar iko.

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron, ya ce gwamnatin Gaddafi ta yi mummunan sabawa kudurin Majalisar dinkin Duniya. Ya yi nuni da rahotanni daga birnin Misrata da ke karkashin ikon ‘yan tawaye da ke cewa dakarun da ke biyayya ga Gaddafi sun cigaba da harbi daga labe suna barin fararen hula kwance jina-jina har sai sun mutu. Y ace sun katse hanyoyin kai kayan abinci da ruwa da wutar lantarki don matsa musu su mika wuya.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, tace sabon kudurin Majalisar Dinkin Duniya ya amince wa kasashe su samar da kayan yaki ga ‘yan tawaye, koda yake ba a yanke shawarar yin hakan ba. Takwaranta na Faransa, Alain Juppe, yace a shirye Faransa ta ke ta shiga tattaunawa kan yadda za a samar da kayan yaki ga mayakan da ke adawa da Gaddafi.

XS
SM
MD
LG