Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mario Monti Ne Zai Zama Sabon Frayim Ministan Kasar Italiya


Mario Monti wanda zai zama sabon frayim ministan kasar Italiya
Mario Monti wanda zai zama sabon frayim ministan kasar Italiya

Masanin tattalin arziki Mario Monti ne zai shugabanci sabuwar gwamnatin kasar Italiya

Sabon Frayim Ministan kasar Italiya, masanin tattalin arziki Mario Monti, yace zai gaggauta kafa sabuwar gwamnati, a kokarin da zai yi na fitar da kasar daga matsalar bashi, wadda ita ce ta ukku a girman tattalin arziki a yankin takardar kudin Euro.

Mr.Monti, tsohon kwamishinan saka idanu kan harakokin tattalin arzikin Tarayyar Turai, yayi wannan furuci ne da yammacin jiya Lahadi bayan da shugaban kasar Italiya Giorgio Napolitano ya zabe shi ya zama frayim minista.

Dole sai ya gabatarwa Mr.Napolitano sunayen ministocin gwamnatin shi kafin a rantsar da shi. Ana kyautata cewa a yau Litinin zai bayyana wadanda ya zaba.

Mr.Monti ya samu goyon bayan manyan jam'iyyun hamayya da kuma wasu 'yan jam'iyyar PDL mai mulki ta tsohon frayim minista Silvio Berlusconi.

Ba a taba zaben Mr.Monti ya rike wani mukami a kasar Italiya ba kuma ba ya cikin kowace jam'iyyar siyasar kasar Italiya. Zai shugabanci kasar har zuwa lokacin da za a yi zabe mai zuwa a shekarar 2013.

Sabuwar gwamnatin na fuskantar kalubalen aiwatar da gagaruman matakan tsaurin da majalisar dokoki ta zartas a makon jiya da nufin rage tulin bashin da ake bin kasar. Shugabannin Tarayyar Turai sun yi na'am da labarin nada Mr.Monti, suka ce wata alama ce mai karfafa guiwa, amma kuma sun yi alkawarin cewa za su ci gaba da saka ido akan al'amarin na kasar Italiya.

Masu fashin bakin al'amura na fata Mr.Monti zai iya samar da wani yanayin da zai kwantar da hankula a kasar wadda ke kokarin neman mafita daga matsalar tattalin arzikin da tulin bashi ya haifar. A makon jiya yawan bashin Italiya ya kai kololuwar shi. Shugabannin kasar Italiya sun so ne su kafa sabuwar gwamnati kafin budewar kasuwannin hada-hadar kudi a yau Litinin, domin su kara kwantar da hankulan masu saka jari cewa tsarin siyasar kasar Italiya yana tsaye da kakafun shi.

XS
SM
MD
LG