Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Ce A Maida Yaki Da Polio Ya Koma Tun Daga Tushe


Masana daga kasashe, ciki har da Najeriya, sun ce tilas gwamnatoci da hukumomi su dauki matakan samun yardar jama'a da kuma bada muhimmanci ga Polio a rigakafin da aka saba yi

Wasu sabbin kasidun da aka wallafa cikin 'yan kwanakin nan sun shawarci hukumomin kiwon alfiya na duniya da su kawo karshen tsarin yaki da Polio inda shugabanni ke bayarda umurnin komai a kasashen Najeriya, Pakistan da kuma Afghanistan, inda har yanzu wannan cuta ta ke da karfi.

A daya daga cikin kasidun, Seye Abimbola na Hukumar Kiwon Lafiya tun daga tushe ta Najeriya, da wasu marubutan daga kasashen uku sun ce tilas gwamnatoci da hukumomi su dauki matakan samun yardar jama'a, su kuma bayar da muhimmanci ko fifiko ga bayar da rigakafin cutar Polio a lokutan ayyukan rigakafi na yau da kullum da aka saba.

Marubutan suka ce dabarun da ake amfani da su na yaki da cutar a wadannan kasashe uku a yanzu, watakila ba su ne suka dace da yanayin wadannan kasashen ba.

Marubutan suka ce gurin hukumomin kiwon lafiya na duniya na kawar da wannan cuta ta Polio watakila ya rufe musu ido daga irin darussan da aka koya dangane da tsare-tsaren kiwon lafiya na kasashe cikin shekaru 30 da suka shige.

Suka ce, "Za a iya kawar da cutar Polio ce kawai idan aka karfafa tsare-tsaren kiwon lafiya, da kuma sanya hannun jama'a, watau a faro daga kasa, can kasa, maimakon daga sama zuwa kasa. Watakila wannan zai bukaci karin lokaci da karin kudade fiye da wanda aka ware ko ake da su yanzu haka a Najeriya da Pakistan da Afghanistan a saboda yanayin siyasar kasashen,"

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG