Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masanan Lafiya Sun Gargadi Mata Masu Shayar Da Nono


Wata mata tana shayar da yaron ta
Wata mata tana shayar da yaron ta

Masana sun ce uwa mai shayarwa na iya shayar da yaron da ba nata ba, amma sai anyi mata gwajin cutar cida, anga cewa bata da ita tukuna.

Masana sun ce uwa mai shayarwa na iya shayar da yaron da ba nata ba, amma sai anyi mata gwajin cutar cida, anga cewa bata da ita tukuna.

Masanan lafiya guda uku, Dr. John Egbuta, Dr. Bisola Animashaun, da Dr. Alfred Dion sune suka bada wannan shawara a wata ganawa da ‘yan jarida a lagos.

Dr. Egbuta, ma’aikaciyar sashin abinci da kungiyar UNICEF a lagos, tace yara ne suka fi samun ribar shan mama, kuma babu wata matsala ko illa mace ta ba jaririn da ba nata ba nononta idan bukata ta tashi muddar ba a riga an yaye jaririn ba.

A cikin bayanin ta, Dr. Egbuta tace, tilas ne a yiwa macen da zata shayar da dan da ba nata ba gwajin cutar cida sosai, domin wannan ce cutar da zata iya zama da cutarwa a maimakon gyara ga jaririn idan ya kasance macen da ta bashi nonon tana dauke da cutar kanjamau ba tare da an sani ba.

Ta kuma kara cewa, madarar nono, madara ce. Tana da amfani kwarai da gaske ga yaro, saboda wani lokaci idan uwar ta rasa ranta wajen haihuwa, ana iya sa kakar yaron ta bashi mama.”

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG