Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masanin Kimiyyar Karkashin Kasa Ba-Amurke Bai Yi Nasara Ba a Karar Da Ya Daukaka

Jakadan Amurka a China Jon Huntsman ke magana da manema labarai a harabar kotun a birnin Beijing
Jakadan Amurka a China Jon Huntsman ke magana da manema labarai a harabar kotun a birnin Beijing

Wata kotun daukaka karat a China ta tabbatar da hukuncin da aka zartas kan wani mai ilimin kimiyyar yanayin karkashin kasa wanda ake zargi da laifin tara bayanai game da bangaren main a China.

Wata kotun daukaka karat a China ta tabbatar da hukuncin da aka zartas kan wani mai ilimin kimiyyar yanayin karkashin kasa wanda ake zargi da laifin tara bayanai game da bangaren main a China.

Kotun ta Beijing a yau Jumma’a ta ki amincewa da daukaka karar da Xue Feng ya yi kan hukuncinsa na daurin shekaru 8 da wata kotu ta zartas masa a watan Yulin day a gabata. Xue wanda ba-Amerike ne dan asalin China, an kama shi ne a watan Nuwamban 2007 bayan ya yi yinkurin sayar da bayanai kan bangaren mai na China. Xue dai na aiki ne a wani kamfanin makamashi da kuma kwararru kan harkar mai mallakin wasu Amurkawa a lokacin da aka kama shi.

Lauyan Xue y ace a baya bayanan da ake takaddama akansu na nan a kasuwa, an maida su wasu abubuwan sirri ne bayan da Xue ya same su.

Jakadan Amurka a China Jon Huntsman ya halarci zaman kotun nay au Jumma’a. Ya gaya wa manema labarai a harabar kotun cewa ya yi takaici sosai da hukuncin, to amman y ace dama abu ne mai yiwuwa

Huntsman ya yi kira ga gwamnatin China ta saki Xue ba tare da bata lokaci ba bisa dalilin tausayi.

XS
SM
MD
LG