Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masarautar Kwantagora Ta Yi Taron Wanzar Da Zaman Lafiya


Masu sallah a wani Masallaci
Masu sallah a wani Masallaci

Sarkin Sudan na Kwantagora, Alhaji Sa'idu Namaska, ya roki masu wa'azi da su daina zagin wasu malaman don kawai fahimtarsu ba iri daya ba

Mai martaba Sarkin Sudan na Kwantagora, Alhaji Sa'idu Namaska, ya roki malamai masu wa'azi, da su guji zage-zage da cinna wutar gabar wasu wadanda fahimtarsu ba daya ba a duk lokacin da suka zo wa'azi.

Haka kuma, sarkin ya bukaci hakimai da sauran masu sarauta da su tabbatar da cewa sai wadanda suke da sani da kuma izni za abari su yi wa'azi.

Sarkin yana magana ne a gaban dubban jama'a da suka halarci taron kolin zaman lafiya na shekara wanda masarautar ta saba gudanarwa kan addini da kuma ilmi.

Shi ma shugaban kwamitin da masarautar ta kafa domin wayar da kan jama'a game da harkokin addini a kasar Kwantagora, Kanar Sani Bello mai ritaya, ya jaddada muhimmancin ilmi na addini da na zamani a wurin taron, yana mai fadin cewa za a barsu a baya idan ba su dage wajen neman ilmin ba.

Kwamishinan harkokin addini na Jihar Neja, Alhaji Shehu Haruna, yace gwamnatin Jihar ta yi murna da irin wannan taro kuma tana bayar da cikakken goyon bayanta. Yayi kira ga sauran masarautu na jihar da su yi koyi da irin wannan mataki da masarautar Kwantagora ta dauka.

Wakilin Sashen Hausa, Mustapha Nasiru Batsari, ya aiko da cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG