Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Bada Taimako Sunyi Alkawarin Kauda Cutar Kanjamau, Tarin Fuka, Da Cutar Cizon Sauro


Sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry
Sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry

Malaman lafiya, shugabanin duniya da kuma masu bada taimako daga kewayen duniya sunyi taro domin su tsara taimakon kudi – da kuma su bayyana ci gaban da aka samu a yaki da wadannan cututtukan uku.

Malaman lafiya, shugabanin duniya da kuma masu bada taimako daga kewayen duniya sunyi taro domin su tsara taimakon kudi – da kuma su bayyana ci gaban da aka samu a yaki da wadannan cututtukan uku. Shugabannin suna da burin samun kudi kimanin dala biliyan 15 a shekara domin yaki da cututukan na tsawon shekara uku da karin kimanin dala biliyan $4.6 akan na lokacin baya.

Kasar Amurka tayi alkawarin bada gudummuwar dala biliyan biyar a wannan shiri. Shugaba Barack Obama ya kuma ce Amurka zata kara dala 1 akan kowacce dala biyu da mai alkawari zai bayar. Kasar Faranshi ta kara bayyana cewar zata bada gudummuwar dala biliyan 1.4 akan wannan kudin na tsawon shekara uku. Japan tayi alkawarin dala miliyan 800, kasar Birtaniya dala biliyan 1.6 da kuma Kanada miliyan 612.

A cikin wadanda suka je taron, mai kudi Billgates na kungiyar Bill da Melinda Gates sunyi alkawarin bayarda miliyan 500 awannan lokacin.

Yayinda yake jawabi a tattaunawar masu bada taimakon, sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry ya nanata mahimmancin cigaba da wannan taimaiko kuma ya baiyyana cigaban da aka samu akan cutar kanjamau, cutar cizon sauro da tarin Fuka. Yace godiya ga masu bada wannan taimako, yana rage yaduwar cutar kanjamau da ake yaki da ita.

Yace “Wani labari ne mai sosa zuciya, yayinda yake Magana kan nasarorin da aka cinma tare cikin kokarin mu na lafiya na duniya. Kuma wani labari ne na yadda duniya ta taru wuri daya ta taimaki mutane kashi 40 da suka karu wajen karbar maganin kanjamau a shekarun da suka wuce. Wani labari ne na kokarin duniya na raguwar kashi 50 na mutanen dake mutuwa ta dalilin cutar tarin fuka zuwa shekara 2015. Labari ne kuma na raguwar cutar cizon sauro a sassa na duniya wanda ya kai ga raguwar mutuwa zuwa kashi uku.”

Wasu mahallata taron sun goyi bayan abinda Kerry. Kerry ya fada da suka hada da Ministar kudi ta Nigeriya, Ngozi Okonjo Iweala wadda tace taimakon da kungiyoyi masu zaman kansu da gwamnatocin kasashe suka yi ya ceci rayukan miliyan mutane a duk kashen duniya daga cututtuka ukun. Da yawa a Afrika, wannan na nufin aiki wajen rage yaduwar cutar kanjamau.

A Nigeriya, tace fiye da mutane miliyan ke karbar maganin rage karfin cutar kanjamau, an sami Karin kimanin kashi bakwai bisa shekarar bara. Hakanan kimanin mataye masu ciki 700,000 suka sami koyarwa akan kiyayewar yaduwar cutar kanjamau daga uwa zuwa danta.

Ngozi tace Nigeriya tana kokarin cigaba kan yaki da cutar cizon sauro. Shugabannin lafiya sun karfafa wuraren yin magani da wurin gwaji, kuma sun bada rigar sauro miliyan 57 domin kiyaye kamuwa da cutar cizon sauro.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG