Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Ciwon Suga Sun Fi Yawa a Kasashen Afrika


Ana dauki gwajin sugan jini
Ana dauki gwajin sugan jini

Bincike ya nuna cewa ciwon sukari ba cutar masu kudi bace kamar yadda a ke fada a da, amma cuta ce da take kama talakawa da yawa.

Bincike ya nuna cewa ciwon sukari ba cutar masu kudi bace kamar yadda a ke fada a da, amma cuta ce da take kama talakawa da yawa. Bincike ya nuna cewa, mutane hudu cikin biyar (kashi 80 cikin dari) na wadanda suke dauke da cutar sikari a duniya suna rayuwa a kasashe masu talauci, bisa ga binciken kungiyar kula da cutar sikari ta duniya (IDF).

Rahoton kungiyar da aka fitar cikin makon da ya wuce a Frankfurt, Germany, a wajen taron karawa juna sani na kwana biyu kan yaki da ciwon suga. Masu binciken sun lura cewa yankin Afrika yafi kowanne yanki yawan masu mutuwa da ciwon suga da kashi 81.2% na masu cutar wadda ba’a tantance ba kuma basu san suna da cutar ba.

Kungiyar masu harhada magungunan ciwon sauga da ake kira Sanofi Biopharmaceuticals ce ta shirya taron domin bukin cika shekaru 90 da jinyar ciwon suga da kuma shirye shiryen yin bukin ranar duniya ta bukin cutar sikari na 2014.

Kungiyari tace akwai mutane masu yawa da suke fama da ciwon suga a yankuna da yawa na duniya da suka hada da suka hada da Eurasia, Turkey da tsakiyar yamma, kudancin Asiya, da Afrika. Kamfanin yace mutane miliyan 143 da suke dauke da cutar a duniya suka san suna dauke da cutar suna kumashan magani daga cikin miliyan 371dake dauke da cutar a duniya a cikin wannan shekarar ta 2013.

An kiyasta cewa kimanin mutane miliyan 237 zasu kamu da ciwon suga a wadannan yankunan daga cikin mutane miliyan 552 da zasu kamu da cutar a duniya baki daya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG