Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Neman A Binciki Kisan Gillar Abuja Na Karuwa


Katin shaidar Ashiru Musa wani dan Funtua, Katsina, kuma daya daga cikin wadanda jami'an tsaron Najeriya suka zazzagewa harsashai a Abuja
Katin shaidar Ashiru Musa wani dan Funtua, Katsina, kuma daya daga cikin wadanda jami'an tsaron Najeriya suka zazzagewa harsashai a Abuja

Kungiyoyin fararen hula da na addinai na ta rusawa gwamnatin Najeriya kiran cewa lallai ta gudanar da bincike a kan kashe-kashen Apo a Abuja

Yawan wadanda aka kashe a Abuja na ci gaba da karuwa sanadiyar mutuwar wadanda ke kwance a asibiti su na jinyar raunukan da suka samu lokacin da jami'an tsaron Najeriya su ka yi mu su ruwan wuta a ranar jumma'ar da ta gabata. Wannan al'amari na faruwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkokin fararen hula, da kungiyoyin addinai na Najeriya ke ci gaba da ziyartar sauran wadanda aka harba da ke kwance a asibiti domin su ga halin da suke ciki, kuma su yiwa hukumomin kasar Najeriya matsin lambar cewa lallai sai sun gudanar da bincike a kan wannan al'amari wanda da yawa ke gani tamkar kisan gilla ne jami'an tsaro su ka aikata. Haka kuma kungiyoyin kare hakkokin fararen hula na shirin yin zanga-zanga a Majalisar dokokin Najeriya domin tursasawa 'yan Majalisar su yi muhawara akan batun tare da bude hanyar yin bincike a kai kamar yadda ya kamata. Ga cikakken bayani a cikin rahoton da Nasiru Adamu el-Hikaya ya aikowa Sashen Hausa daga birnin Abuja:


Kiran neman a yi bincike game da kashe-kashen Abuja - 2:50
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG