Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Sayen Dabbobi a Ibadan Sun Ce Sun Yi Tsada


A protester stands with his hands on his head as a cloud of tear gas approaches after a grand jury returned no indictment in the shooting of Michael Brown in Ferguson, Missouri, Nov. 24, 2014.
A protester stands with his hands on his head as a cloud of tear gas approaches after a grand jury returned no indictment in the shooting of Michael Brown in Ferguson, Missouri, Nov. 24, 2014.

Amma masu sayar da dabbobin sun ce sun zabtare musu farashi sosai domin su sayar, ganin cewa ana fama da matsalar kudi ba kadan ba

A garin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, akasarin mutane masu sayen raguna ko shanu domin Sallar layya dake tafe ranar talata, sun koka da cewa farashin dabbobin yayi tashin gwauron zabi fiye da duk shekarun baya.

Da yawa daga cikin wadanda suka tattauna da wakilinmu Hassan Umar Tambuwal, sun ce a shekarar da ta shige, farashin dabbobin bai yi tashi kamar na bana ba, domin ragunan da ake sayarwa Naira dubu 25 zuwa dubu 28 a bana, an saye su a kan naira dubu 18 a shekarar da ta shige.

Sai dai masu sayar da dabbobin sun ce rashin kasuwa ya tilasta musu rage kudaden dabbobin a kan yadda suka fara tallata su. Wani mai sayar da dabbobin yace daga cikin raguna fiye da 200 da ya taho da su, guda 30 kawai ya samu zarafin sayarwa ya zuwa yanzu. Dalili ke nan da ya sa suka fara karya musu kudade.

Ga cikakken bayani a tattaunawar da wakilin namu yayi da masu sayen dabbobin a garin Ibadan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG