Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BORNO: Mata Masu Juna Biyu Sun Sami Tallafi


'Yan gudun hijira kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.
'Yan gudun hijira kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

Kwamitin kula da wadanda suka rasa matsugunansu sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram yAce an kashe naira biliyan uku daga cikin naira biliyan ishirin da biyar da gidauniyar ta sami karbowa daga cikin naira biliyan hamsin da hudu da aka yiwa gidauniyar alkawari

Shugaban kwamitin Farfesa Sunday Ochoche ya bayyana cewa, gidauniyar taba asibitoci biyu a jihar Borno da suka hada da asibitin kwararru da kuma asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, naira miliyan ashirin kowannensu a lokacin da kwamitin ya kai ziyara jihar kwanan baya, domin taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya raunata da suke karbar magunguna a wadannan jihohi.

Farfesa Ochoche yace akwai aiki a gaban gidauniyar tukuru na sake gina gidajen wadanda rikicin kungiyar Boko Haram ya shafa, yace a wannan ziyarar da suka kawo, suna da adadin mata masu juna biyu dari hudu da goma wadanda zasu ba naira dubu goma kowannensu domin su iya kula da kansu yanzu da kuma bayan sun haihu.

Yace baki daya, gidauniyar tana shirin taimakawa mata dubu uku ne a jihar Borno kawai, matan da suka sami tallafin sun bayyana cewa, zasu sayi ragunan suna da kuma muhimman kayayyakin bukata daga cikin tallafin da aka basu.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Bi’u ya aiko daga jihar Borno, Najeriya.

BORNO: An Tallafawa Mata Masu Ciki-2:53"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG