Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matar Gwamnan Jihar Neja Ta Ja Kunnen Alhazan Jihar


Hajiya Jummai Babangida Aliyu ta gargadi alhazan jihar da kada su dauki kayayyaki fiye da kima, fiye da ka'idojin da aka shimfida musu.

Uwargidan gwamnan jihar Neja, Hajiya Jummai Babangida Aliyu, ta shawarci alhazan jihar da su guji daukar kaya fiye da ka'idojin da aka shimfida musu, tana mai fadin cewa akasarin kayayyakin da alhazan suke saya, ana iya samunsu cikin sauki a Najeriya.

A lokacin da ta kai ziyarar gaisuwar Sallah ga alhazan na Jihar Neja a masaukinsu a birnin Makkah, Hajiya Jummai Babangida Aliyu, ta taya alhazan murnar kammala aikin Hajji cikin nasara tare da fatan Allah Ya karbi ibadarsu.

Amirul Hajj na Jihar Neja, kuma mataimakin gwamnan Jihar, Alhaji Ahmed Musa Ibeto, ya bayyana cewa sun dauki matakai da dama a bana na tabbatar da cewa alhazan jihar ba su gamu da wata matsala a lokacin aikin hajjin ba, kuma sun samu nasarar hakan.

Jami'an sun kai wannan ziyara a daidai lokacin da alhazan jihar ta Neja suke jimamin rasuwar wani mahajjaci guda daga karamar hukumar Chanchaga wanda ya rasu a Makka. Hukumomin Sa'udiyya dai su na binciken musabbabin rasuwarsa.

Ga cikakken rahoton da Mustapha Nasiru Batsari ya aiko daga Makka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG