Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Adamawa Sun Rungumi Sana’ar Kira


Yayin da ake fama da matsalar rashin aikin yi a Najeriya, yanzu haka wasu matasa sun yunkuro a jihar Adamawa, Arewa maso Gabashin Najeriya, inda suka rungumi sana'ar ‘Kira kuma tuni kwalliya ta fara biyan kudin Sabulu.

Hakan na zuwa ne alokacin da hankula suka fara kwantawa biyo bayan nasarar da dakarun Najeriya ke ci gaba da samu kan kungiyar Boko Haram.

Mallam Abubakar Aliyu sarkin Lauje da Usman Yahaya Adamu na daga cikin shugabannin wannan masana’anta, kuma sun bayyana yadda wannan sana’a ke tafiya a yanzu. Ita dai wannan Makera ana kiranta ne Makerar Sarkin Lauje, inda manya da matasa harma da yara ke aiki, haka kuma akwai bangarori da dama cikinta inda ake kere keren kayan amfanin yau da kullum musammam ma kayan noma.

A cewar matasan dake aiki wannan Makera, sunce suna koyon sana’a ne domin samun hanyar dogaro da akai, har ma sun nemi tallafin kayan aiki irin na zamani.

An dai dade ana kira ga matasa domin su rungumi sana’ar hannu domin samun hanyar rage zaman kashe wando da mafi yawan matasan Najeriya ke yi.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG