Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Man Fetur a Najeriya


Layi a gidan mai a Najeriya (fayal)
Layi a gidan mai a Najeriya (fayal)

Ana fuskantar matsalar hauhawar farashin man fetur a Najeriya saboda faduwar darajar Naira.

A cikin dalilan da suka haifar da hauhawar farashin man fetur a Najeriya, wakilin sashin Hausa Mahmud Kwari yayi hira da shugaban kungiyar masu jigilar man fetur Bashir Danmalan inda yake cewa kamar haka.

“Faduwar darajar naira da kuma hauhawar farashin dala wadda ake samu a kwanan baya kan dari da hamsin da biyar, ta koma dari da sittin da takwas daga karshe kuma ta haura zuwa dari da tasa’in da tara. Dan haka masu shigo da man wato kanfanin jigilar man fetur mai zaman kanta dake Lagos taga cewar gibin yayi yawa”.

A cewar shi, dogaro da kasashen waje bazai taba taimakon Najeriya ba, ya kuma kara da cewar gwamnati ta gyara matatun man dake cikin kasar domin samar da saukin wannan matsalar.

Daga karshe kuma ya tabbatar da cewa zargin da ake masu na cewar suna boye mai ba gaskiya bane, kuma a matsayin shi na shugaban kungiyar suna nan suna cigaba da kokarin ganin cewar duk abinda ya samu za’a fitar da shi domin jama’a su samu.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

XS
SM
MD
LG