Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsayar Gwamnatin Amurka A Kan Bada Takardun Izinin Shiga Kasar


Ma’aikatar tsaron Amurka ta umurci daukacin ofisoshin jakadancin kasar manya da kanana da ke duk fadin duniya, da su tabbatar sun kula da irin mutanen da ke bukatar bincike mafiya tsauri na takardar izinin shigowa Amurka.

Haka kuma umurnin ya bukace su da su binciki bayanan hanyoyin sadarwar na zamani wadanda suka nemi takardar iznin shigowa Amurka, musammam ma wadanda ake tuhuma suna da nasaba da ta’addanci ko kuma daga kasashen da ke karkashin barazanar kungiyar ISIS.

Yanzu haka dai Ministan harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya aike wa ofisoshin jakadancin Amurka sakonnin ta kebabbun kafafen sadarwa na diflomasiyya, inda ya bukaci da su shirya ganawa ta jami’an tsaro da bayanan sirri, wadanda za su bullo da tsarin binciken duk wasu da ake ma ganin masu bukatar tantancewa mai tsauri.”

Domin koda mai neman takardar ya cimma sharuddan da aka gitta, duk da haka suna bukatar a kara tsananta bincike akan su. Idan ta kama ma ana iya hana musu.

Wannan shine alamun farko na tsananin binciken masu neman shigowa Amurka wanda shugaba Trump, yayi alkawari lokacin yakin neman zabe. Yanzu ya zame wajibi ofisoshin jakadancin Amurka, su fadada binciken su ga masu neman izinin shigowa, domin samun cikakken bayanin ko shigowar tasu ka iya zamewa barazana ga Amurka, da Amurkawa ko kuma a’a.

Da farko dai kanfanin dillacin labaran Reuters ne ta fara yayata wannan labarin, wanda ya janyo suka daga jama’a, dama kungiyoyi da suke sukar Shugaba Trump, na nuna banbanci ga Musulmai ta hanyar umurnin nan nasa da hana wasu ‘yan kasashe 6 wadanda galibin su musulmai ne shigowa Amurka, amma kuma aka takawa umurnin birki, Jiya kungiyar kare hakkin bani adama ta Amnesty international ta bukaci a baje wadannan umurnin a fai-fai kowa ya gani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG