Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Abuja Sun Zabura Wajen sa Ido Akan Tsaro


Masu aikin lafiya suke jinyar weani daga cikkinwadanda harin da aka kai Nyanya ya rutsa da su.
Masu aikin lafiya suke jinyar weani daga cikkinwadanda harin da aka kai Nyanya ya rutsa da su.

Sakamakon haka an kama wani mutum da yake niyyar dasa bam a wani masallaci a unguwar Garki.

Rundunar 'Yansandan Najeriya a Abuja ta tabbatar da labarin kama wani mutum d a yayi yunkurin dasa bam a wani masallacin jumma'a dake unguwar Garki a Abuja. ASP Altine Daniel ce ta tabbatar da wannan labari, baya ga haka ma rundunar tana binciken wani jami'in soja kan zargin kisan wata ba fulata na mai sayar da nono a unugwar Dede.

Wani mazaunin unguwar Garki Sani Tela, ya gayawa Sashen Hausa na Muriyar Amurka cewa mutumin yana tambayar mutane inda masallacin Izala take a unguwar, da suka lura da take takensa suka gane cewa, akwai alamun bashi da kyakkawar niyya a zuciya.

Da yake magana kan wannan al'amari babban sakataren kungiyar Jama'atul Nasril Islam Dr. Khalid Aliyu yayi kira ga limamai d a shugabbannin addini su dage wajen yawaita addu'o'i da zummar Allah ya tona asirin dukkan wadanda suke haddasa wannan fitina.

A nasa bangaren babban jami'i a helkwatar kiritoci ta CAN Pastor Simon Dolli, ya tsame addini daga cikin dalilanda suke haddasa fitina. Yace addini tamkar makaranta ce, inda mutum mai 'yaya biyu ko wanne yake zuwa wata makaranta dabam, amma da zarar sun komo gida zasu ci gaba da zama 'yan uwa.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG